IQNA

Kin Amincewa Da Saka Musulunci Ya Zama Kundin Tsarin Mulki A Sudan

23:42 - August 04, 2019
Lambar Labari: 3483911
Bangaren kasa da kasa, jam'iyyar congress ta tsohon shugaban Sudan Umar Albashir bata amince da yin watsi da musulunci a cikin kundin tsarin mulkin kasar ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna, jaridar Quds Alarabi ta bayar da rahoton cewa, jam’iyyar Congress ta tsohon shugaban kasar Sudan ta nuna rashin amincewa da matsayar da bangarorin soji da jam’iyyun siyasa masu neman canji suka cimmawa, kan rashin sanya muslunci ya zama abin dogaroa  cikin kundin tsarin mulkin kasar.

Bayanin jam’iyyar ya ce, abin da bangarorin suka cimma matsaya a kansa ya sabawa abin da ke cikin kundin tsarin mulkin kasar na 2005, wanda ya wajabta cewa dole ne addinin mulsunci ya zama abin dogaro na karshe  a cikin kundin tsarin mulkin.

Jam’iyyar ta Congress dai ta bayyana cewa ba ta da shawar shiga cikin gwamnatin rikon kwarya da za a kafa wadda bangarorin soji da kuma jam’iyyun siyasa masu neman sauyi suka cimmawa, amma a za ta shiga zabe a  lokacin da za a gudanar da zabukan ‘yan majalisar dokokin kasar.

A ranar Asabar da ta gabata ce, wakilin kungiyar tarayyar Affrika mai shiga tsakani a  Sudan Muhammad Alhassan Lubat ya sanar da cewa, bangarorin siyasar kasar sun cimma matsaya kan kafa gwamnatin rikon kwarya.

3832402

 

captcha