IQNA

22:56 - August 10, 2019
Lambar Labari: 3483933
An gudanar da taken bara’a ga mushrikai bayan karanta sakon jagoran juyin juya halin musulunci a filin Araf a yau Asabar.

Majiyar muryar jumhuriyar musulunci ta Iran daga filin Afarah ya bayyana cewa a taken na bara’a ga Mushrikai a yau Asabar a filin na arafah ya hada da taken “Allah ya kawo karshen Amurka” da kuma “Allah ya kawo karshen Isra’ila”.

Labarin ya kara da cewa banda mahajjata Iraniyawa, da dama daga cikin mahajjatan wasu kasashen duniya sun halarci taron na karanta sakon jagoran juyin juya halin Musulunci Aya. Sayyeed Aliyul Khamina’e da kuma taken na bara’a daga baya.

A cikin taron ne wadanda suka halarci taron bara’ar suka karanta wasu al-amura masu muhimmanci guda 5, wadanda suka hada da daukar al-amarin palasdinawa a matsayin al-amari mafi muhimmanci da ya shafi al-ummar musulmi a halin yanzu.

Hadin kan al-ummar musulmi da kuma kira ga kungiyoyin kasa da kasa wadanda suka hada da majalisar dinkin duniya na su himmatu da taimakawa raunanan mutane a duniya daga cin zalin manya-manyan kasashen duniya.

Daga karshe Karanta addu’ar Arafah na Imam Husain na daga cikin ayyukan ranar Arafa da aka gudanar a filin arafa a yau Asabar.

3834003

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، muhimmanci ، Arafah
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: