IQNA

23:53 - August 19, 2019
Lambar Labari: 3483965
Ilhan Omar da Rashida Tlaib sun yi kira zuwa ga kawo karshen mamayar Isra’ila a yankunan Falastinawa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, Ilhan Omar da Rashida Tlaib ‘yan majalisar dokokin Amurka mata musumi, sun bayyana takacinsu kan mamayar yankunan Falastinawa da Isra’ila take yi, tare da bayyana fatansu na ganin cewa an ‘yantar da yankunan Falastinawa daga mamayar Isra’ila.

A cikin bayanan da suka rubuta a shafukansu na zumunta twitter, dukkanin ‘yan majalisar biyu sun bayyana cewa, sun yi burin ziyartar yankunan Falastinawa da Isra’ila ta mamaye a gabar yamma da kogin Jordan, amma Isra’ila ta hana su bizar shiga.

Jama’a da dama a kasar Amurka da kuma kasashen larabawa, suna ci gaba da mayar da martani, dangane da matakin da Isra’ila ta dauka na hana wadannan ‘yan majaisar dokokin Amurka musulmi shiga Falastine, musamman ma ganin cewa daya daga cikinsu ‘yar asalin falastine ce.

 

3835926

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: