IQNA

23:54 - August 21, 2019
Lambar Labari: 3483974
Bangaren kasa da kasa, artabu tsakanin dakarun Hadi kuma masu samun goyon bayan UAE a Yemen.

Kamfanin dillancin labaran iqna, jaridar Quds Alrabi ta bayar da rahoton cewa, wasu dakaru masu samun goyon bayan UAE sun kaddamar da mummunan farmaki kan dakaru masu biyayya ga shugaban Yemen mai murabus Hadi Abdu Rabbuhu Mansur agarin Abyan da ke kudancin Yemen.

Rahotanni sun ce an fara kaddamar da farmaki ne a kan babban ofishin ‘yan sanda da ke garin na Abyan, wanda ke karkashin dakarun Hadi, daga nan kuma fada mai tsanani ya barke tsakanin bangarorin biyu.

Ya zuwa daren jiya dai rahotanni na cewa an kashe dakarun Hadi masu yawa a garin na Abyan, kuma dakarun masu biyayya ga UAE, sun shimfida ikonsu a mafi yawan sassa na birnin.

Tun a cikin kimanin makonni biyu da suka gabata ne aka fara wani gumurzu mai a garin Aden da ke kudancin kasar Yemen, tsanani tsakanin dakarun Hadi Abdu rabbuhu Mansur, wanda yake samun goyon bayan masarautar Al Saud, da kuma wasu dakarun da suka balle masa, wadanda su kuma suke yin biyayya ga gwamnatin hadaddiyar daular larabawa.

A halin yanzu dai dakarun da suke yin biyayya ga UAE ne suke rike da ikon birnin Aden, bayan fatattakar dakarun Hadi masu samun goyon bayan masarautar Al saud.

3836396

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: