IQNA

23:56 - August 28, 2019
Lambar Labari: 3483995
Bangaren kasa da kasa, dubban mutanen Kashmir ta Pakistan sun gudanar zanga-zangar adawa da India.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin Daily Sabah cewa, an gudanar da wannan jerin gwano a garin Muzaffar Abad na Kashmir, inda aka yi tir da abin da India take yi kan yankin Kashmir da ke akrkashinta.

Wannan zanga-zanga ta zo ne kwana daya bayan furucin da firayi ministan kasar wanda ya bayyana cewa dole ne a dauki mataki na ganin an cewa an takawa India burki kana bin da take tafkawa a kasar al’ummar Kashmir.

A ranar 27 ga watan Satumba ne firayi ministan kasar Pakistan zai gabatar da bayani a  gaban babban taron majalisar dinkin duniya, inda zai yi bayani kana bin da yake faruwa a Kashmir.

Batun rikicin Kashmir dai ya kawo rashin jituwa tsakanin Pakistan da India.

3838240

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، burki ، India ، bayani
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: