IQNA

23:49 - September 02, 2019
Lambar Labari: 3484010
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Musawi ya bayyana hare-haren jiragen yakin saudiyya kan gidan kason Dhamar a kasar Yemen da cewa abin Allawadai ne.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a birnin Tehran, Abbas Musawi ya bayyana cewa, gidan kaso wuri ne inda ake kula da wasu mutane da suke a matsayin amana, wanda kare irin wadannan wurare wajibi wajibi ne ga kowa.

Ya ce kaddamar da hare-haren a kan wannan gidan kaso ya tabbatar da cewa wadanda suke yaki da al’ummar kasar Yemen bas a kiyyae wata kaida ko doka ta kasa da kasa, domin kuwa tun kafin hakan dama sun saba kai irin wadannan hare-harea wurare da aka haramta kai musu hari a lokacin yaki.

Ya ce masu kai hare-haren suna samun wadannan muggan makamai ne daga gwamnatin Amurka da kuma wasu daga cikin kasashen turai da suke da’awar kare hakkokin ‘yan adam da kare rayukan fararen hula, wanda hakan ke tababtar da cewa suna da hannu a kisan fararen hula a kasar Yemen.

 

3839124

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Abbas Musawi ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: