IQNA

23:54 - September 07, 2019
Lambar Labari: 3484024
Bangaren kasa da kasa, ana gudanar da tarukan ashura a cibiyar Alkausar da ke birnin hague na kasar Holland.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakato daga shafin QAF cewa, bisa ga alada kamar yadda aka saba  akowace shekara ana gudanar da tarukan ashura a cibiyar Alkausar da ke birnin hague na kasar Holland  tare da halartar jama’a.

Bayanin ya ce akan fara ne da gabatar da karatun kur’ani mai tsarki kafin shiga cikin bayanin abubuwan da suka shafi ashura a kowace shekara da shahasar Imam Hussain (AS) da sauran wadanda suke tare da shi.

Daga cikin masu gabatar da karatun kur’ani ‘yan kasar Ho;;and da kuma wasu daga kasashen turai, daga ciki akwai Jalil Ahmad Khairpour, Ali Alturaihi, Masih Nu’aimi, da Reza Qhorbani.

 

3840734

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Holland ، ashura ، juyayi
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: