IQNA

23:57 - September 08, 2019
Lambar Labari: 3484031
Bangaren kasa da kasa, an bude bababn baje kolin kur’ani mai tsarki na kasada kasa a birnin Jakarta na kasar Indonesia.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar ad rahoton cewa, a babban baje kolin kur’ani mai tsarki na duniya da ake gudanarwa a Jakarta Indonesia an bayar da kyautar kwafi dubu na na kur’ani ga amsu duba baje kolin.

Dukkanin kwafin kur’anin da aka bayar wadanda aka tarjama nea  cikin harshen Indonesia, wanda cibiyar buga kur’ani ta sarki fahad ta dauki nauyi bugawa da kuma rabawa ga mutanen Indonesia.

Tuna  ranar Laraba da ta gabata ce aka fara gudanar da wanann baje koli na kasa da kasa a birnin Jakarta fadar mulkin kasar Indonesia tare da halartar mutane daga bangarori daban-daban na kasar da kuma kasashen ketare.

 

3840846

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: