IQNA

23:37 - September 14, 2019
Lambar Labari: 3484048
Bangaren siyasa, Sayyid Abas Musawi ya mayar da martani kan matakin da gwamnatin Canada ta dauka akan kaddarorin Iran.

Kamfanin dillancin labaran iqna, gwamnatin kasar Iran ta yi allawadai da matakin da gwamnatin kasar Cadana ta dauka, bisa bukatar wata kotu a kasar, na saida wani gini mallakin gwamnatin kasar Iran, don bawa wasu da ta kira wadanda ayyukan ta’addancin kasar Iran ya shafa”

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Abbas Muaswi ya kara da cewa dole ne gwamnatin kasar Canada ta soke wannan cinikin kuma da mayarwa gwamnatin kasar Iran ginin, idan bata yi haka ba, Iran zata dauki matakan da suka dace, a sannan gwamnatin Ottawa Canada ta yi koka da kanta.

Kamfanin dillancin labaran Global News ta bada labarin cewa gwamnatin kasar Canada ta saida wani gini mallakin ofishin yada al’adun kasar Iran da ke kasar, sannan ta mika dala miliyon 30 ga wasu ya kasar ta Iran da sunan kudaden fansa don cutar das u da kasar Iran ta yi.

3841849

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: