IQNA

23:55 - September 18, 2019
Lambar Labari: 3484062
Kungiyar tarayyar turai ta yi tir da matakin da gwamnatin Isra'ila ta dauka na ci gaba da gina matsugunnan yahudawa a cikin yankunan Falastinawa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoto, ami magana da yawun babbar jami’a mai kula da harkokin wajen kungiyar tarayyar turai ta bayyana cewa, ci gaba da gina matsugunnan yahudawa da Isra’ila ke yia  cikin yankunan Falastinawa abin ban takaici da Allawadai.

Ta ce dole ne Isra’ila ta dakatar da gina matsugunnan yahuadawa a cikin yankunan Falastinawa da ke gabar yamma da kogin Jordan, domin yin hakan ya sabawa dukaknin dokoki da ka’idoji na duniya.

Wannan sanarwa na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan wani furuci da firayi ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi ne, da ke cewa idan ya lashe zabe zai hade yankunan Falastinawa na gabar yamma da kogin Jordan da kuma Isra’ila.

Yanzu haka dai akwai matsugunnan yahudawa kimanin dari biyu da hamsin da Isra’ila ta gina  a cikin yankunan Falastinawa da ke gabar yamma da Kogin Jordan, inda yahudawa ‘yan share wuri zauna kimanin dubu dari hudu suke rayuwa a cikin wadannan matsugunnai.

3843177

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، tarayyar turai ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: