IQNA

Rauhani: babu Tattaunawa Karkashin Takunkumi A Kan Iran

22:50 - September 25, 2019
Lambar Labari: 3484085
Bangaren siyasa, shugaba Ruhani ya bayyana cewa kasar Iran ba za ta taba amincewa da tattaunawa da Amurka a karkashin takunkumai ba.

Shugaban kasar Iran Dr Hassan Ruhani ya bayyana cewa kasar Iran ba za ta taba amincewa da bude tattaunawa da Amurka a karkashin takunkuman tattalin arziki mafi tsanani da ta dorawa kasar ba.

A bangaren yaki da ayyukan ta’addancinn kuma shugaban ya bayyana cewa kasar Iran tare da hadin kai da kasashen yankin gabasa ta tsakiya sun sami nasarar kawo karshen kungiyar Daesh a wadannan kasashe, don haka kasar Iran tana daga cikin kasashen da suke yakar ayyukan ta’addanci a duniya.

Ruhani ya kara da cewa, amma kasar Amurka bayan shekaru 18 da mamayar kasar Afganistan ta kasa kawo karshen ayyukan ta’addanci a kasar.

Har’ila yau dangane da harkokin tsaro a mashigar ruwa ta Hurmuz da kuma Tekun Oman masu muhimmanci ga kasashen yankin da kuma sauran kasashen duniya, shugaban ya gabatar da wani shiri wanda ya bashi suna “Fata” da kuma “Shirin Tabbatar Da Tsaron Mashigar Hurmuz”.

Dangane da wannan shirin shugaban ya bukaci dukkan kasashen yankin tekun fara su tattauna a tsakaninsu don samar da zaman lafiya a yankinsu.

Dr Ruhani ya kara da cewa duk wani kawance karkashin shugabancin Amurka ko wasu kasashen waje ba zasu taba samar da zaman lafiya a yankin mashigar ruwa ta Hurmuz ba”

Dangane da takunkuman tattalin arzikin da kasar Amurka ta dorawa kasar Kuma shugaban kasar ta Iran ya ce, abinda Amurka take yi shi ne ake kira “ta’addancin tattalin arziki” don ta takurawa mutanen kasar Iran kimani miliyon 83, ta hanasu hakkinsu hatta na samun maganin cutattukan da suke fama da su.”

Har’ila yau shugaban yayi maganar yerjejeniyar Nukliyar kasar ta shekara ta 2015, wacce Amurka ta yi watsi da ita kimani shekara guda da rabid a ya gabata, da kuma rashin ciki alkawullan 11 wadanda kasashen turai suka yiwa kasar Iran bayan ficewar Amurka daga yerjejeniyar, duk wadannan sun taru sun tilastawa Iran daukar matakai na jingine wasu yerjejeniyar ta 2015, mataki, mataki, don bawa sauran kasashen damar cika alakwulan da suka dauka, mai yuwa idan sun cika su  Iran ta sake dawowa domin yin aiki da bangarorin da ta yi watsi da su.

3845023

 

 

captcha