IQNA

23:50 - September 28, 2019
Lambar Labari: 3484096
Bangaren kasa da kasa, bangarori daban-daban na kasa da kasa sun maar da martani kan matakan murkushe masu bore a Masar.

Kamfanin dillancin labaran iqna, sharin arabi 21 ya bayar da rahoton cewa, dubban al’ummar sun fito a wasu manyan biranan kasar Masar da suka hada da Alkahira, Jiza, Alaqsar, Alminya da sauransu, domin neman shugaban kasar Abdulfattah Sisi ya sauka daga shugabancin kasar.

An gudanar ad irin wannan zanga-zanga a wasu kasashe da suka hada da Jamus da kuma Faransa, inda dubban misrawa mazauna wadannan kasashe da ma wasu kasashen turai, suka tarua  gaban ofisoshin jakadancin Masar, suna kira ga Sisi da ya gaggauta sauka daka kan kujerar shugabancin kasar.

A bangaren guda kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya gargadi gwamnatin Masar kan daukar duk wani mataki da za hana jama’a bayyana ra’ayinsu ta hanyar zanga-zangar lumana.

A nata bangaren kungiyar Afuwa ta duniya ta bayyana matakan da gwamnatin Masar ta dauka na hada dubban mutane isa wuraren gangami da cewa keta hurumin al’ummar kasar ne.

Haka nan kuma kungiyar ta kirayi gwamnatin Masar da ta saki mutane kimanin 1900 daga cikin masu zanga-zangar lumana da ta kame.

Tun a makon da ya gabata ne aka fara bore a Masar, bayan bankado wata almundahana da Abdulfattah Sisi yake da hannu dumu-dumu a cikinta.

3845302

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: