IQNA

23:55 - October 01, 2019
Lambar Labari: 3484107
Bangaren kasa da kasa, jagoran kungiyar Ansarullah a kasar Yemen ya bayyana cewa babbar manufarsu ita ce tabbatar da zaman lafiya a Yemen.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran sputnik ya bayar da rahoton cewa,a  lokacin da yake zantawa da manzon musamman na majalisar dinkin duniya a kasar Yemen, jagoran kungiyar Ansarullah Abdulmalik Huthi ya bayyana cewa, borinsu shi ne ganin al’ummar emen sun rayu cikin aminci da zaman lafiya.

Ya ce ganawarsa da manzon musamman na mjalisar dinkin duniya ta yi armashi matuka, kuma ganawar ta mayar da hankali ne kan batun sakin fursunonin yaki tsakaninsu da Saudiyya da ‘yan korenta, da kuma batun kawo karshen yakin da makiya kasar suke kaddamarwa a kanta, gami da ayyukan taimako ga wadanda suke bukatar agajin gaggawa sakamakon yakin.

A nasa bangaren babban manzn musamman na majalisar dikin duniya a Yemen Martin Griffiths ya bayyana cewa, sun na’am da shawar da Mahdi Mashat shugaban majalisar koli ta gudanar da kasar Yemen ya gabatar, inda y ace za su dakatar da kai harin ramuwar gayya kan Saudiyya, amma bisa sharadin cewa dole ne ita ma ta dakatar da hare-haren da take kaiwa kan al’ummar kasar Yemen.

 

http://iqna.ir/fa/news/3846550

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Yemen ، Alhuthi ، Saudiyya
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: