IQNA

22:20 - October 02, 2019
Lambar Labari: 3484111
Bangaren kasa da kasa, an bude ajujuwan wucin gadi na koyon karatun kur’ani a kasar Zimbabwe.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, an bude wasu ajujuwan wucin gadi na koyar da karatun kur’ani mai tsarki ga kananan yara a birnin Harare fadar mulkin kasar Zimbabwe.

Karamin ofishin jakadancin kasa Iran a kasar Zimbabwe ne ya dauki nauyin wanann shiri, domin yada koyarwar kur’ani mai tsarkia  tsakanin musulmin kasar marassa rinjaye, wanda kuma shirin ya samu karbuwa daga musulmin kasar.

Baya ga haka kuma akwai wasu shirye-shiryen na asar kur’ani, wanda ake bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka nuna wazo.

 

3846521

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، zimbabwe ، harare ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: