IQNA

Musulmin Australia Sun Yi Kira Da A Kafa Doka Hana Nuna Musu Kyama

23:27 - October 03, 2019
Lambar Labari: 3484116
Bangaren kasa da kasa, musulmin kasar Australia sun yi kira ga mahukuntan kasar kan a kafa dokar da za ta hana nuna musu kyama.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na Sunday Morning ya bayar da rahoton cwa, kungiyoyi da cibiyoyin musulmin kasar Australia sun kiray Fira ministan kasar da ya dauki mataki na ganin an kawo karshen nuna musu kyama da wasu suke yi a kasar.

Cibiyoyi da kungiyoyi da kwamitocin musulmin Australia 150 ne suka fitar da bayani na hadin gwiwa wanda  acikinsa suke yin kira da a kafa doka a hukumance wadda za ta haramta keta alfarmar addinai ko cin zarafin mabiya wasu addinai a kasar.

Daga ciki akwai kwamitin limaman kasar, da kuma majalisar koli ta musulmin kasar, da kuma ‘yan asalin kasar Lebanon mazauna Australia da saransu.

Jami’ar Charls ta kasar Australia na shirin fitar da wani rahoto kan yadda ake nuna wa musulmin kasar wariya da cin zarafinsu ta hanyoyin sadarwa na yanar gizo, wanda ya karu a cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan.

3846936

 

 

 

 

 

captcha