IQNA

22:25 - October 12, 2019
Lambar Labari: 3484147
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da wani baje kolin kayan al’adu na muuslmin duniya a jihar Chicago ta Amurka.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga tashar IBC Chicago cewa, a jiya an fara gudanar da wani baje kolin kayan al’adu na muuslmin duniya a cibiyar Sabeel Center a jihar Chicago ta Amurka, mai take daga Amurka zuwa Zajbar.

Wannan baje koli ya kunshi nuna kaya al’adu namusulmi a kasashen duniya daban-daban, kama daga yanayin tufafinsu, abinci, kayan fasahar rubutu da zane-zane, kayan kida, wuraren tarihi da sauransu.

A cikin watan Fabrairun shekara ta 2016 ne aka fara gudanar da irin wannan baje koli.

A daren jiya n aka fara gudanar da wannan baje koli, kuma zai ci gaba har zuwa 22 ga watan Disamban karshen wannan shekara.

3849228

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Chicago ، Amurka ، aladu
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: