IQNA

22:59 - October 21, 2019
Lambar Labari: 3484176
Bangaren kasa da kasa, firayi ministan Sudan ya bayar da umarnin kafa kwamitin binciken kisan masu zanga-zanga.

Kamfanin dillancin labaran iqna, firayi ministan kasar Sudan Abdullah Hamduk ya sanar da cewa, za a kafa wani kwamiti da zai gudanar da bincike kan kisan masu zanga-zangar da aka gudanar a kasar Sudan.

Shafin yada labarai na Ahram ya bayar da rahoton cewa, firayi ministan Sudan Abdullah Hamduk ya fadi cewa za su kafa wani kwamiti da zai gudanar da bincike kan kisan masu zanga-zanga, wanda zai kunshi mambobi bakawai.

Ya ce daga cikin mambobin akwai babban alkali guda da kuma manyan lauyoyi guda biyu, haka nan kuma ma’aikatun cikin gida, tsaro da kuma shari’a za su bayar da nasu wakilan a cikin kwamitin, wanda suke da lokaci zuwa watanni shida domin kammala duk wani bincike kan wannan batu.

Tun bayan da al’ummar kasar Sudan suka fara zanga-zangar bore ga gwamnatin Albashir, jami’an tsaro sun yi amfani da karfi wajen tarwatsa jama’a, kamar yadda kuma bayan kifar da Albashir soji ma sun yi amfani da karfi wajen kashe daruruwan masu adawa da salon mulkinsu.

Jagororin gamayyar kungiyoyi da jam’iyyun siyasa a kasar Sudan ne suka bukaci da a gudanar da sahihin bicike na gaskiya a kan hakikanin abin da ya faru, tare da kame masu laifi.

 

3851331

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: