IQNA

22:37 - October 22, 2019
Lambar Labari: 3484180
Bangaren kasa da kasa, dubban mutane sun fito a biranan kasar Sudan suna kira da a rusa jam’iyyar Albashir.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin tashar Russia Today cewa, a jiya dubban mutanen kasar Sudan sun fito a birane daban-daban na kasar domin yin kira da a rusa jam’iyyar Albashir hambararren shugaban kasar.

Rahoton ya ce masu zanga-zangar sun fito a mafi yawan biranan kasar ta Sudan dauke da kwalaye da aka yi rubutu a kansu, kan cewa dole ne a kawo karshen jam’iyyar ‘yan kama karya, kuma a hukunta wadanda suka kasha masu zanga-zangar neman ‘yanci.

Haka nan kuma masu jerin gwanon sun rika yin kira ga mahukuntan kasar das u tabbatar da cewa kotu ta yi adalci wajen hukunta Albashir da kuma sauran wadanda suke da hannu a cikin murkushe masu zanga-zanga a lokacin Albashir.

Yanzu haka dai hambararren shugaban kasar ta Sudan yana fuskantar shari’ar mallakar makudan daruruwan miliyoyin daloli da hanyar haram.

3851576

 

 

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: