IQNA

MDD: Akwai Bukatar Mayar Da Batun Myanmar Zuwa Kotun ICC

23:51 - October 26, 2019
Lambar Labari: 3484194
Majalisar dinkin duniya ta bukaci a mayar da batun kisan kiyashin ‘yan kabilar Rohingyaa Myanmar zuwa kotun manyan laifuka ta duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Yanghee Lee manzon musamman ta majalisar dinkin duniya kan rikicin Myamnar ta bayyana cewa, dole ne a mayar da batun Myamnar zuwa kotun duniya domin hukunta masu a hannu a kisan kiyashi kan musulmin Rohingya.

A lokacin da take zantawa da manema labarai a cikin ginin majalisar dinkin duniya, Yanghee Lee ta bayyana cewa, ta mika rahoto na musamman da ta harhada dangane da kisan kiyashin da aka yi wa musulmi ‘yan kabilar Rohingyaa kasar Myanmar.

Baya ga haka kuma ta ce ta hada wasu rahotanni dangane da irin mawuyacin halin da aka jefa dubban daruruwan musulmin na Rohingya a cikin kasarsu, da kuma wuraren da aka tsugunnar da su musamman acikin kasar Bangaladesh.

Ta ce akwai wadanda suka tafka manyan laifuka yaki acikin gwamnatin Myanmar a cikin wannan lamari, kuma dole ne a kai batun a gaban kotun duniya domin hukunta su.

Tun a ranar 25 ga watan Agustan 2017 ne jami’an sojin kasar Myanmr da kuma ‘yan addinin buda masu tsatsauran ra’ayi suka fara yin wani kisan kiyashiakan musulmi ‘yan kabilar Rohingya, wadanda galibinsu suke zaune ajihar Rakhin, inda aka kona kauyukansu fiye da 350.

Yanzu haka dai adadin musulmin Rohingya da suka yi gudun hijira da aka tsugunnar da su a kasar Bangaladesh ya kai mutane dubu 725, da suka hada da mata da kananan yara.

3852243

 

 

captcha