IQNA

22:59 - November 07, 2019
Lambar Labari: 3484230
Bangaren kasa da kasa, mahukuntan Girka sun daure mai bayar da fatawa na kasar kwanaki 80 a gidan kaso.

Kamfanin dillancin labaran iqna, jaridar Hurriat ta bayar da rahoton cewa, Ibrahim Sharif mahukuntan Girka sun zarge shi da karbe mukamin mai bayar da fatawa ga muuslmin kasar.

Shi dai mazaunin kasar ne a yankunan da musulmi ‘yan asalin Turkiya suke, kuma shi ne yake a matsayin babban malaminsu.

An taba yi masa rin wannan zargi a 1999, amma kungiyar tarayyar turai ta hana a daure shi.

A sheara ta 1990 ne muuslmin yankin suka zabe shia  matsayin babban mai basu fatawa.

Tun a ckin shekara ta 1913 daular Usmaniya da gwamnatin Girka ska cimma yarjejeniya kan cewa muuslmin kasar Girka ne suke da hakkin ayyayana mai bayar da fatawa.

Amma a shekarar 1991 gwamnatin Girka ta yi watsi da wannan yarjejeniya, inda ta kafa dokar cewa dole ne gwamantin kasar ce za ta zaba wa musulmin kasar wanda zai rika basu fatawa.

 

3855306

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: