IQNA

23:13 - November 10, 2019
Lambar Labari: 3484237
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana kawancen Amurka a tekun fasha da cewa Ba shi da alfanu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a jiya kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Abbas Musawi ya fitar da wani bayani, wanda a cikinsa yake mayar da martani kan kafa kawancen Amurka da sunan tabbatar da tsaro a cikin tekun fasha, inda ya ce manufar hakan ita ce kare muradun Amurka da kuma ci gaba da kara tsunduma yankin cikin tashin hankali.

Ya ci gaba da cewa, suna yin kira ga sauran kasashen larabawa na yankin tekun fasha das u dawo cikin hayyacinsu, su fahimci cewa ba manufar Amurka ba ce ta tabbatar musu da tsaro, manufar Amurka ita ce wawushe kudinsu da kaddarorinsu da sunan tabbatar musu da tsaro.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, kasar Iran ita ce kasar da take da gabar ruwa mafi tsawo a cikin tekun fasha, kuma ita ce take baiwa dukkanin yankunta kariya , a kan haka hada karfi da karfe tsakanin dukkanin kasashen yankin domin gudanar da ayyukan hadin gwiwa, shi ne zai tabbatar da tsaro a yankin baki daya.

 

3855728

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: