IQNA

Mutane Miliyan Daya Sun Ziyarci Lambun Kur’ani A Dubai

15:44 - November 18, 2019
Lambar Labari: 3484252
Bangaren kasa da kasa, mutane kiamnin miliyan daya ne suka ziyarci lambun kur’ani a cikin watanni 7 da suka gabata a Dubai.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga mujallar Gulf Today cewa, akalla mutane kiamnin miliyan daya ne suka ziyarci lambun kur’ani a cikin watanni bakawai tun bayan bude shia  birnin Dubai na hadaddiyar daular labarawa.

An gina wannan karafaren lambun kur’ani ne a cikin wani fili mai fadin hekta 64, wanda aka gina shi a bangarori 12, kamar yadda kuma aka samar da nau’oin tsirrai 45 da aka ambata a cikin kur’ani.

Haka nan kuma an samar da wasu abubuwa da suke nuni da wasu ababen da aka yi ishara da su a kin kur’ani mai sarki, kamar sandar annabi Musa (AS) da kuma wasu abubuwa na tarihin annabawa da al’ummomin da suka gabata.

Babbar manufar samar da wannan wuri dai ita ce kara jawo hankulan masu yawan bude ido zuwa birnin na Dubai, musamman ma masu son sanin abu dangane da kur’ani.

3857890

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha