IQNA

16:59 - November 19, 2019
Lambar Labari: 3484254
Kakakin gwamnatin Iran ya bayyana cewa hakkin al'ummar kasar ne su yi korafi, amma barnata dukiyar kasa ba korafi ba ne laifi ne.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, kakakin gwamnatin kasar Iran ya mayar da martani kan goyon bayan da hukumomin Amurka ke bawa masu tayar da tarzoma da cinna wuta a dukuyoyin gwamnati da mutane a kasar Iran, inda ya ce babu wani abu da muke jira daga saktaren harakokin wajen kasar Amurka Mike Pampeo face goyon bayan masu tayar da tarzoma.

Yayin da yake katsa landan kan harakokin cikin gida na kasar Iran, sakataren harakokin wajen Amurka Mike Pampeo ya nuna goyon bayansa ga masu tayar da tarzoma a gariruwa daban-daban na kasar ta Iran.

Yayin da yake gabatar da taron manema labarai bayan zaman gwamnati da ya gudana a wannan Litinin, kakakin gwamnatin kasar Iran Ali Rabi'i ya bayyana cewa magabatan kasar Amurka da suka kakabawa al'ummar Iran takunkumin zalinci, a yanzu sun fito fili ba kunya suna nuna goyon bayansu ga masu tayar da tarzoma a kasar.

Yayin da yake ishara kan irin karyayyakin da gwamnatin Amurka ke shirgawa al'ummarta musaman a lokacin zabe, Rabi'i ya bayyana cewa duk kasar da Amurka ta shiga tayi katsa landan a harakokin al'amuran cikin gidanta to ba za ta samu ci gaban da take bukata ba.

Kakakin gwamnatin jamhoriyar musulinci ta Iran ya tabbatar da cewa al'ummar Iran nada masaniya da irin makircin kasar Amurka, kuma juriya da gwagwarmayar al'umma zai kawar da wannan makarkashiya ta makiya.

Rabi'i ya ce masu zanga-zanga nuna adawa da karin farashin man fetir daban suke da masu tayar da tarzoma, kuma manufarsu shi ne hana sauraron bukatar masu zanga-zanga, amma basirar al'ummar Iran ya sanya suka raba sahunsu da masu tayar da tarzoma.

 

3857926

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: