IQNA

18:16 - November 28, 2019
Lambar Labari: 3484281
Yahudawan sahyuniya 1400 ne suka kutsa kai a cikin hubbaren annabi Yusuf (AS) a gabashin Nablus.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, shafin yada labarai na almasirah ya bayar da rahoton cewa,a  jiya dandazon Yahudawan sahyuniya sun kutsa kai a cikin hubbaren annabi Yusuf (AS) a gabashin Nablus da ke gabar yamma da kogin Jordan.

Rahoton ya ce yahudawan sun keta alfarmar wannan wuri ne bisa hujjar gudanar da tarukansu na addinin yahudanci.

Sai dai a nasu bangaren matasan falastinawa da dama ne suka nuna rashin amincewa da keta alfarmar hubbaren annabi Yusuf (AS), amma jami’an tsaron Isra’ila sun yi arangama da su.

Haka nan kuma ra hoton ya kara da cewa, jami’an tsaron na Isra’ila wadanda suke bayar da kariya ga yahudawa masu tsatsaan ra’ayi da suka kutsa kai cikin hubbaren annabi Yusuf, sun yi harbi da bindiga da kuma jefa barkonon tsohuwa domin tarwatsa falastinaan.

3860160

 

https://iqna.ir/fa/news/3860160

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: