IQNA

15:27 - December 18, 2019
Lambar Labari: 3484330
Bangaren shari’a a Afrika ta kudu na ci gaba da bincike kan harin da aka kai wa wani masallaci a garin Durban.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, babban alkalin alkalan Afrika ta kudu ya ce suna ci gaba da bincike kan harin da aka kai wa masallacin Imam Hussain (AS) a garin Durban na kasar.

An bukaci mutumin da ake zargi wato Farhad Hummar da ya bayar da sautinsa domin bincike, domin kwatanta shi da sautin da aka dauka jim kadan bayan kai harin, wanda ya yi sanadiyyar rasuwa Muhammad Abbas Asup limamin masallacin.

Ana tsare da Hummar da wasu mutane 11 da ake zargin suna da hannua  wannan harin, da ma wasu tuhumce-tuhumcen da suke alakanta su da ‘yan ta’adda.

3864877

 

 

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: