IQNA

2:38 - December 25, 2019
Lambar Labari: 3484344
Shugaban cibiyar ahlul bait (AS) ya bayyana cewa sheikh Zakzaky na bukatar magani a waje.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, Ayatollah Redha Remazani bababn sakataren cibiyar Ahlul bait (AS) ta duniya ya bayyana cewa, akwai bukatar a bayar da dama domin yi wa sheikh Ibrahim Zakzaky magani a waje.

Malmin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai yau, inda ya bayyana cewa; batun Sheikh Zakzaky batu ne na ‘yan adamtaka, a kan haka ne suke kokarin ganin an samu mafita dangane da lamarin nasa.

Ya ci gaba da cewa, bisa la’akari da bayanai da kwararrun likitoci suka bayar dangane da yanayin jikinsa, akwai buakatar a samu wata dama ta duba shia  waje domin ya samu cikakkiyar kulawa, ta yadda za a iya magance matsalolin da suke damunsa sanadiyyar harbinsa da harsasai.

Dangane da abin da suke kan wannan batu ya bayyana cewa, akwai hanyoyi na tuntuba dangane da yadda za a samu mafita kan wannan lamari, kuma hakan ba yin shigar shugula ba ne a cikin harkokin Najeriya, domin kuwa batu ne ‘yan adamtaka.

Ya ce suna da fatan ganin an samu daidaiton fahimta, ta yadda hakan zai iya bayar da damar sake fitar da shi domin ci gaba da yi masa magani, wanda shi ne abin da yake da muhimmanci a halin yanz dangane da makomar lafiyarsa.

Haka nan kuma baya ga kokarin da ya ce cibiyar ahlul bait (AS) tana yi kan wannan batu, ya yi ishara da kokarin da da kuma ya ce wasu bangarorin suna yi, na tuntubar gwamnatin Najeriya da kuma tattaunawa kan yadda za a warware matsalar.

A kwanakin baya ma kakkain ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar muslunci ta Iran ya bayyana cewa, akwai tuntuba tsakanin gwamnatocin kasashen biyu kan batun Sheikh Zakzaky.

Inda ya ce akwai kyakkayawar alaka ta diflomasiyya tsakanin kasashen biyu, kuma suna tattaunawa kan yadda sheikh Zakzaky zai samu damar samun magani a waje, wanda kuma suna da kyakkyawar fata kan cewa gwamnatin Najeriya za ta amince da hakan.

Ayatollah Ramezani daga karshe bayaninsa ya bayyana cewa, yana yin kira da a sau kwarrun likitoci domin wasu daga malamai wadanda suke fama da irin wanann matsala ta siyasa, da suka hada da Sheikh Isa Kasim na Bahrain, da kuma sheikh Hussain Ma’atuq na kasar Kuwait.

Za a iya duba hotunan zaman a nan:- click here

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3866301

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: