IQNA

1:03 - December 26, 2019
Lambar Labari: 3484346
Bangaren kasa da kasa, musulmin Amurka sun taiamka ma kiristoci da abinci a daren kirsimati.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, shafin yada labarai na Fox 40 ya bayar da rahoton cewa, cibiyar ayyukan alhairi ta musulmi mai suna American Muslims Voices ce ta gudanar da wannan aiki.

Kimanin shekaru bakawai kenan wanann cibiya tana gudanar da irin wannan aiki a kowace a daren sallar kirsimati.

Khalid Said shugaban cibiyar ya bayyana cewa, annabi Isa (AS) daya ne daga cikin manyan manzanin Allah da suke da matsayi a cikin addinin muslunci, saboda haka taimaka ma kiristoci marassa galihu a daren haihuwarsa aiki ne na alhairi mai kyau da musulmi suke yi.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3866480

 

 

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، kiristoci ، kirsimat ، Amurka
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: