IQNA

Za A Bude Wasu Cibiyoyin Bincike Na Addini A Kasar Masar

15:38 - January 01, 2020
Lambar Labari: 3484365
Bangaren kasa da kasa, za a bude wasu cibiyoyin bincike na addinin muslunci a kasar Masar.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, Darul Fatwa babbar cibiyar bayar da fatawar addinin musunci a Masar ta sanar da cewa, yanzu haka ana shirin za a bude wasu cibiyoyin bincike na addinin muslunci a kasar.

Ibrahim Najm, babban mashawarci ga shugaban cibiyar bayar da atawa a Masar ya bayyana cewa, za a kaddamar da wadannan cibiyoyi nea  cikin wannan sabuwa shekara ta 2020 da muka shiga a yau.

Ya ci gaba da cewa, manufar hakan ita ce samar da wani tsari na musamman wajen bincike, wanda zai taimaka ma masana, musamman ma wadannan suke gudana da bincike kan wasu muhimman lamrra da suka shafi addini, ko kuma masu rubutun furoje na jami’oi.

Babbar manufar hakan ita ce, domin wannan tsari ya taimaka wajen fito da hakikanin koyarwar addinin muslunci, ganin yadda masu kyamar muslunci suke ta hankoron ganin sun bata sunan addinin muslunci, sakamakon abin da wasu jahilai wadanda ba su san addini ba suke aikatawa.

Daga daga cikin abin ake amfani da shi wajen bata sunan adinin muslunci shi ne batun ta’addanci, alhali babu ta’addanci a cikin addinin muslunci, kuma ‘yan ta’adda ba su wakiltar usulunci, kuma musulmin duniya ba su yarda da abin da yan ta’ada suke aikatawa da sunan musulunci ba.

 

https://iqna.ir/fa/news/3868146

 

captcha