IQNA

10:45 - January 08, 2020
Lambar Labari: 3484394
Donald Trump ya yi Magana kan batun harin ramuwar gayya da Iran ta kai kan sojojin Amurka a Iraki.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, tashar Sky News Arabic ya bayar da rahoton cewa, Trump ya yi Magana kan hare-haren a kan sojojin kasarsa.

A cikin bayanin nasa wanda ya biyo bayan kai harin daukar fansa da dakarun Iran suka yi, Trump ya bayyana cewa, suna yin dubi kan irin hasarorin da harin ya jawo musu.

Haka nan kuma Trump ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu bisa ga labarin da suke da shi, shi ne cewa Iran ta kaddamar da hari ne a sansanonin sojin Amurka guda biyu a cikin kasar Iraki, kuma har yanzu dai babu wata babbar asara da suka ji labarin an samu a sansanin sojin na Amurka, saboda haka za su yi bayani daga bisani.

Kafin wannan lokacin dai Trump ya yi barazanar cewa, matukar Iran ta saki ta mayar da martani kan Amurka a kan abin da ya faru, to za ta fuskanci mummunan hari daga Amurka.

 

https://iqna.ir/fa/news/3870133

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: