IQNA

12:40 - January 09, 2020
Lambar Labari: 3484398
Jagoran juyin juya halin mulunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei na ci gaba da halartar zaman karbar gaisuwar shahadar Kasim Sulaimani.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, jagoran juyin juya halin mulunci na Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei tare da manyan jami’an gwamnati da manyan jami’an tsaron kasar, suna ci gaba da halartar zaman karbar gaisuwar shahadar Kasim Sulaimani a  Husainiyar Imam Khomenei (RA) da ke birnin Tehran.

Wanann zaman karbar gaisuwa dai zai ci gaba har zuwa ranar Asabar, inda jagoran zai halarci zaman da za a yi a hubbaren Sayyid Ma’asumah da ke birnin Qom.

Baya ga jami’an gwamnati, dubban mutane ne daga sassa na birnin Tehran suke halartar zaman gaisuwar.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3870387

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: