IQNA

22:39 - January 15, 2020
Lambar Labari: 3484417
Sayyid Muqtada daya daga cikin masu fada a ji a kasar Iraki, ya kirayi miliyoyin al’ummar kasar da su gudanar da zanga-zanga kan Amurka.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin nasa, Muqtada sadr ya bayyana cewa, sakamakon yadda Amurka take ta yin taurin kai wajen kin aiwatar da kiran al’ummar Iraki, kan neman ta fitar da sojojin daga kasar.

Yana kira da a gudanar da gagarumar zanga-zanga a fadin kasar domin yin tir da Allawadai da kasantuwar sojojin Amurka a Iraki.

Ya ce sakamakon irin matakan da Amurka take dauka na haifar da matsaloli na tsaroa cikin kasar Iraki, da kuma kudirin da majalisar dokokin kasar ya amince da kan wajabcin ficewar sojojinta daga kasar, ya zama wajibi ta fice daga kasar Iraki ba tare da bata lokaci ba.

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3871683

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: