IQNA

21:48 - January 20, 2020
Lambar Labari: 3484434
Harin ‘yan ta’addan Daesh ya tilasta mutane kimanin 7000 tserewa daga yankunansu a Nijar.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, shafin yada labarai na News18 ya bayar da rahoton cewa, hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya ta bayar da rahoton cewa kimanin mutane 7000 sun tsere daga yankunansu bayan ‘yan ta’adda da ya kashe sojojin Nijar 89 a’yan kwanakin da suka gabata.

Bayanin hukumar ya ce bayan kai harin na garin Chinegodar wanda ke tazarar kilo mita 20 daga iyakokin Nijar da Mali, dubban mutane fararen hula da suka hada har da ‘yan gudun hijira kimanin 1000 sun tsere.

Haka nan kuma hukumar ta kara da cewa, dukkanin mutanen da suka gudu suna da matukar bukatar taimakon gagawa musamman na abinci da kayayyakin bukatar rayuwa.

A makon da ya gabata ne Daesh ta dauki alhakin kai harin na ranar 9 ga watan Janairu, a kan barikin sojin Nijar, wanda ya yi sanadiyyar kashe sojojin kasar.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3872726

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: