IQNA

21:59 - February 01, 2020
Lambar Labari: 3484473
An samar da wani tsari na na’ura mai kwakwalwa da zai taimaka masu ziyarar lambun Quranic Park a cikin harsuna 8.

Kmafanin dillacin labaran IQNA, domin saukaka ma masu ziyarar lambun quranic park a Dubai an samar da wani tsari na na’ura mai kwakwalwa da zai taimaka masu ziyarar lambun.

Rahoton ya ce wannan tsari wanda yake da sunan Quranic Park yana amfani da harsuna 8, da suka hada da Larabci, Ingilishi, Indiyanci, yaren China, Faransanci, Rashanci, Spaniyanci, da Italiyanci.

Sa’anan kuma tsarin yana da hanyoyi na tarjama a cikin harsunan Ingilishi da kuam harshen Urdu, wanda idan aka saka Kalmar a cikin google tarjamar za ta fita a cikin harsunan biyu.

Lambun Quranic Park dai yana nuan abubuwa da dama da suka zo cikin kur’ani mai tsarki da suak shafi tsirai da itace da dangoginsu, kamar yadda kuma ake saka alluna masu dauke ad ayoyin da suke dauke bayanin wadannan tsirrai ko itace.

Haka nan kuma wannan tsari yana taimakawa wajen gano inda lambun yake a cikin sauki.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3875538

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: