IQNA

23:49 - February 04, 2020
Lambar Labari: 3484483
Ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ta mayar da martani kan kungiyar tarayyar turai dangane matsayin da ta dauka kan shirin Trump.

kamfanin dillancin labaran IQNA, shafin yada labarai na Ynet news ya bayar da rahoton cewa, ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ta fitar da bayani wanda a cikinsa take mayar da martani kan, kan kalaman jami'in harkokin wajen tarayyar turai, wanda yake cewa cewa yunkurin Isra'ila na sake mamaye wasu yankunan falastinawa da ke gabar yamma da kogin Jordan ya saba wa doka.

Bayanin ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ya ce, matsayar da babban jami'in kungiyar tarayyar turai mai kula da harkokin siyasar wajen kungiyar ya dauka kan batun mamaye yankunan gabar yamma da kogin Jordan, hakan abin ban takaici ne, kuma barazana ce ga Isra'ila.

Josep Borrell babban jami'i mai kula da harkokin siyasar wajen kungiyar tarayyar turai ya yi suka kan shirin Trump da ake kira yarjejeniyar karni ta zaman lafiya tsakanin falastinawa da Isra'ila.

Inda ya bayyana cewa wannan shiri ya yi hannun riga da abin da yake rubuce a cikin dokokin kasa da kasa, kuma kungiyar tarayyar turai ba za ta taba amincewa da mamayar yankunan falastinu na shekara ta 1967 ba.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3876608

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: