IQNA

23:48 - February 09, 2020
Lambar Labari: 3484500
Shugaban kwamitin gudanawa na kungiyar tarayyar Afrika ya bayyana cewa, kasantuwar babu falastinawa a cikin yarjejeniyar ba za ta kai labari ba.

Kamfanin dilalncin labaran IQNA, shugaban kwamitin zartarwa na kungiyar tarayyar Afrika Musa Faki ya fadia  wurin taron kungiyar tarayyar Afirka ewa, yadda aka tsara abin da ake kira da yarjejeniyar hakan babu abin da zai haifar sai kara tsanantar rikici tsakanin Isra’ila da falastinawa.

Ya ce kungiyar tarayyar Afrika ba za taba amincewa da irin wanann shiri ba, wanda zai kara yawan tasin tashina tsakanin falastinawa da kuma Isra’ila.

Musa ya kara da cewa, babban abin da tarayayr Afrika ta damu da shi, shi ne samar da wani tsari wanda zai samar da sulhu a tsakanin falastinawa da Isra’ila.

Daga karshe ya bayyana cewa yarjejeniyar kan wanza da zaman lafiya tsakanin falastinawa da Isra’ila amma ba tare da falastinawa a cikin yarjejeniyar ba, ba ta da ma’ana.

 

https://iqna.ir/fa/news/3877692

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: