IQNA

23:56 - February 10, 2020
Lambar Labari: 3484507
Shugabannin Afirka sun yi watsi da abin da ake kira yarjejeniyar karnia amansu na birnin Addis Ababa a kasar Habasha.

Kamfanin dillancin labaran IQNA,

A jiya Lahadi ne shugabannin kasashen nahiyar Afirka da su ke taron shekara-shekara a birnin Adis Ababa na kasar Habasha su ka nuna kin amincewarsu da shirin shugaban kasar Amurka Donald Trump tare da yin tir da shi, da kuma bayyana shi a matsayin wanda ba halartacce ba.

Bugu da kari shugabannin na kasashen nahiyar Afirka sun bayyana cikakken goyon bayansu ga manufar al’ummar Palasdinu.

Shugaban cibiyar tarayyar ta Afirka Musa Faki Muhammad ya fada wa manema labaru cewa; Shirin wanda aka gabatar da shi a karshen watan Janairu yana a matsayin ci gaba da take dokokin majalisar Dinkin Duniya masu yawa da kuma na Tarayyar Afirka.

Har ila yau Musa Faki ya ce; An tsaro yarjejeniyar ne ba tare da tuntubar bangarorin duniya ba, don haka ta take hakkokin Palasdinawa

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3878032

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: