IQNA

23:59 - February 10, 2020
Lambar Labari: 3484508
Adadin sojojin Amurka da suka samu matsalar kwakwalwa sakamakon harin Iran a sansaninsu da ke Iraki yana karuwa.

Kamfanin dillancin labaran A, kamfanin dillacin labaran reauters ya bayar da rahoton cewa, jami’an gwamnatin Amurka sun bayyana cewa, rundunar sojin kasar tana ci gaba da tantance adadin sojojin da suka samu raunuka sakamakon harin Iran.

Rahoton ya ce wani babban jami’in gwamnatin Amurka ya tabbatar wa da kamfanin dillancin labaran reuters cewa, adadin sojojin da suka samu matsalar kwakwalwa sakamakon harin Iran ya haura 100.

Ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon dai ba ta ce komai ba dangane da rahoton na reuters, amma koa  kwanakin baya ta fitar da wani bayani da ke tabbatar da cewa wasu daga cikin sojojin kasar sun samu raunuka sakamakon harin na Iran, daga ciki kuma har da wadanda suka samu matsalar kwakwalwa.

Iran dai ta mayar da martani ne da makamai masu linzami kan sansanonin sojin Amurka a Iraki, biyo bayan kisan Kasim Sulaimani, da Abu Mahdi Al-muhanddis da Amurka ta yi.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3878039

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: