IQNA

23:54 - February 11, 2020
Lambar Labari: 3484511
Bangaren kasa da kasa, tun da safiyar yau ne miliyoyin jama’a suka gudanar da bukukuwan cika shekaru 41 da juyin juya hali a Iran.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, an gudanar da jerin gwano mafi girma a birnin Tehran fadar mulkin kasar ta Iran a yau, tare da halartar manyan jami’an gwamnatin kasar, kamar yadda kuma miliyoyin jama’a suka halarta, inda aka gabatar da jawabai a dandalin ‘yanci da ke tsakiyar birnin.

Shugaban kasar ne Rauhani ne ya gabatar da jawabi, a gaban dimbin jama’a, inda ya jaddada cewa kasar tana nan daram kan bakanta na kin mika wuya ga manufofin ‘yan mulkin mallaka.

Kafofin yada labarai da daman a ciki da wajen kasar sun bayar da rahotanni kai tsayea okacin gudanar da gangamin, inda tashar Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayar da rahoton cewa, a wannan karo tutocin kasar Iran da hotunan Kasim Sulaimani ne aka yi ta dagawa a wurin gangamin.

Haka nan kuma kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya bayar da cikakken rahoto a kan tarukan da aka gudanar a kasar ta Iran a yau a birnin Tehran da sauran biranan kasar.

Kamar yadda kamfanin dillancin abaran Associated press ma ya bayar da rahoton da ke taron na yau yana daga cikin manyan taruka da aka taba yi kasar.

Baya ga haka ‘yan rahoto daga tashohin yada labarai da daman a duniya da suka halarci taron na yau, sun bayar da rahotanni masu kama da juna kan fitowar miliyoyin al’umma domin tunawa da ranar ta cikar juyin juya hali shekaru arba’in da daya a kasar.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3878113

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: