IQNA

23:54 - February 12, 2020
Lambar Labari: 3484515
Wani karamin yaro dan shekaru hudu ya bayar da kyautar kwafin kur'ani ga gwamnan lardin Asyut na Masar a lokacin bude baje kolin kayan al'adu.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, Abram Romani Zarif wani yaro ne dan shekaru hudu da haihuwa wanda ya halarci baje baje kolin kayan a’adu a lardin Asyut tare da mahaifiyarsa, inda ya bayar da kyautar kwafin kur’ani ga Isam Sa’ad gwamnan lardin an Asyut a taron baje kolin.

Wannan baje koli dai ana gudanar da shi ne har tsawon mako guda, inda ake baje kayan al’adu da ake sana’antawa da hannu.

Mafi yawan kayan da aka bajea  wurin kaya ne da daliban dami’a ta lardin Asyut da kuma jami’ar Azhar ska sana’anta, wanda jama’a suke zuwa dubawa, da hakan ya hada da jami’an gwamnati da kuam sauran mutanen gari, gami da masu yawon bude ido a kasar ta Masar.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3878351

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Masar ، Asyut ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: