IQNA

Pompeo Ya Tattauna Da Jami'an Saudiyya Kan Iran

23:58 - February 19, 2020
Lambar Labari: 3484540
Tehran - (IQNA) sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya tattauna tare da jami'an gwamnatin Saudiyya kan Iran a ziyarar da ya kai kasar.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya tattauna tare da jami'an gwamnatin Saudiyya kan Iran da kuma matakai na hadin gwiwa da za su ci gaba da dauka tare domin fuskantarta.

A cikin rahoton na kamfanin dillancin labaran reuters, Pompeo ya sheda wa ‘yan jarida da suke tare da shi cewa, a ziyarar tasa a Saudiyya zai kwashe tsawon kwanaki biyua  kasar yana tattaunawa da manyan jami’an gwamnatin kasar, da suka hada da sarki Salman bin Abdulaziz, da kuma yarima mai jiran gado Muhammad Bin Salman.

Pompeo ya sheda cewa, mafi yawan abubuwan da zai tattauna da jam’ian gwamnatin Saudiyya a kan kasar Iran ne, domin su kara hada karfi da karfe tsakanin Amurka da Saudiyya wajen ganin sun shiga kafar wando daya da Iran.

Ya ce manufofin Amurka da Saudiya daya ne a kan kasar Iran, a kan haka dole ne kasashen biyu su yi aiki tare kan hakan, wanda kuma dama tuni suna yi, kuma za su kara himma ne kawai kan hakan.

Masana da dama dai sun yi imanin cewa, Amurka ta mayar da kasar ta Saudiyya tamkar wata saniyar da ake tatsa a duk lokacin da bukatar hakan ta taso kamar yadda Trump ya fadi hakan da bakinsa.

Masanan suna ganin cewa Amurka tana yin amfani da sunan Iran wajen tsorata kasashe irin su Saudiyya wajen tatsar makudan daruruwan biliyoyin daloli, da sunan za ta ba su kariya daga duk wata barazana ta Iran.

 

 

3880054

 

 

captcha