Tashar Alalam ta bayar da rahoton cewa, Muhammad Ali Alhuthi shugaban majalisar juyin juya hali a kasar Yemen, ya bayyana cewa tsayin daka da al'ummar kasar Yemen suka yi tare da hada kai wajen tunkarar masu mummunan kudiri kan kasar, sako ne mai matukar muhimmanci ga dukkanin al'ummomin duniya, da hakan ya hada har da makiyan kasar ta Yemen.
Ya ce tun shekaru biyar da suka gabata, Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa tare da taimakon Amurka da Burtaniya, suke kaddamar da hare-hare ta sama da kasa da ta ruwa, tare da killace kasar Yemen baki daya, tare da hana shigo da abinci da magunguna da makamashi a cikin kasar, bayan kisan dubban fararen hula mata da kananan yara, amma duk da haka al'ummar Yemen ba su mika kai ga manufofin 'yan mulkin mallaka da 'yan korensu ba.