IQNA

22:58 - March 10, 2020
Lambar Labari: 3484608
Tehran (IQNA) Shugaban kasar China Xi Jinping ya bayyana cewa, sun samu nasarar shawo kan yaduwar cutar corona a  kasar.

Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa ya bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake gudanar da wata ziyara a jiya a birnin Wuhan na kasar China wanda daga nan cutar corona ta fara, shugaban kasar ta China Xi Jinping ya bayyana cewa, sun samu nasarar dakile yadda cutar corona take yaduwa a baya a cikin sauri a  kasar.

Ya ce tasirin da cutar corona ta yi a kan tattalin arzikin kasar ba mai jimawa ne ba, domin kuwa tuni suka fara daukar matakan cike gibin da hakan ya haifar.

Shugaban kasar ta China ya kara da cewa, bisa la’akari da raguwar wadanda suke kamuwa da cutar a Wuhan, da kuma yawan wadanda suka warke daga cutar, za a iya cewa an samu babban ci gaba wajen wajen yaki da cutar, da kuma kokarin dakile ta.

 

3884490

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: China ، cutar corona ، yaduwa ، dakile ، kasar ، Wuhan
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: