IQNA

23:57 - March 18, 2020
Lambar Labari: 3484632
Tehran (IQNA) Tayyib Abdulrahim sakataren gwamnatin Falastinawa ya rasu asafiyar yau.

Jaridar Hadas da ake bugawa a Falastinu ta bayar da rahoton cewa, Tayyib Abdulrahim babban sakataren gwamnatin Falastinawa, kuma ammba na kungiyar Fatah ya rasu a yau bayan fama da rashin da lafiya.

An haife shia  sheakara ta 1944 a garin Ambata da ke cikin yankin Tulkaram.

Shi da ne ga Abdulrahim Mahmud, fitaccen dan gwagwarmayar Falastinu, wanda ya yi shahada wajen kare garin Shajara daga mamayar yahudawa.

Tayyib Abdulrahim na daga cikin wadanda suka fara shiga cikin kungiyar Fatah tun 1965 a lokacin da yake jami’ar Kahira.

Ya kasance daya daga cikin na hannun damar Malam Yasir Arafat a lokacin da yake a raye.

3886276

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Fatah ، falastinu ، malam Yasir Arafat ، shahada ، kungiyar
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: