IQNA

Akwai Bukatar Taimaka Ma Gaza Domin Yaki Da Corona

23:52 - March 31, 2020
Lambar Labari: 3484671
Tehran (IQNA) kakakin magatakardan majalisar dinkin duniya yace  yankin Zirin Gaza na bukatar taimakon gaggawa ta fuskar kiwon lafiya.

A jiya ne mai magana da yawun babban sakataren majalisar dinkin duniya Stephane Dujarric ya bayyana cewa, yankin zirin Gaza na daga cikin wuraren da al’ummominsu suke cikin mawuyacin hali, a kan haka ne babban sakataren majalisar dinkin duniya ya bukaci gaggauta taimaka ma al’ummar yankin a cikin irin wannan yanayi.

Ko a ranar Laraba da ta gabata ce babban sakataren majalisar ya kaddamar da wani shiri na hada kudi dala biliyan 2 domin taimaka ma kasashe masu rauni, domin yaki da cutar corona, inda ya bayyana yankin zirin Gaza a matsayin daya daga cikin yankunan da za su samu wannan taimako na majalisar.

Akwai mutane fiye da miliyan biyu da suke rayuwa a yankin Zirin Gaza wadanda Isr’ila ta killace su baki daya, tare da haramta wa kasashe yin mu’amala da su balantana taimaka musu.

Jami’an Gwamnatin Falstinu sun ce ya zuwa yanzu jimillar mutane dari da sha takwas suka kamu da cutar corona a Falastinu baki daya, goma daga cikinsu kuwa suna a zirin Gaza ne da kewaye.

 

3888422

 

 

captcha