IQNA

Saudiyya Ta Bukaci A Dan Dakata Dangane Da Shirye-Shiryen Aikin Hajjin Bana

23:50 - April 01, 2020
Lambar Labari: 3484673
Tehran (IQNA) mahukuntan Saudiyya sun nemi musulmin duniya da su dakatar da shirye shiryen zuwa aikin hajjin bana.

Tashar Sky News ta bayar da rahoton cewa, ministan ma’aikatar kula da aikin hajji da Umara na kasar Saudiyya, ya ce yanke hukuncin aikin hajji yanzu zai zamo aikin gaggawa, a don haka ya bukaci da a dan saurara har a ga abin da  hali ya yi sakamakon halin rashin tabbas da ake ciki game da annobar coronavirus.

Mohammad Benten, ya kara da cewa Saudiyya ta shirya tsaf don gudanar da aikin hajjin, saidai a wannan hali da ake ciki, masarautar Saudiyya na son kare lafiyar musulmi da kuma ‘yan kasar, don haka muka bukaci dukkan ‘yan uwa kasashe dasu dakatar da karbar duk wata kwangila da wani kamfanin shirya aikin hajji.

Kawo yanzu dai hukumomin na Saudiyya ba su tsaida magana ba akan cewa za’a gudanar da aikin hajjin na bana ba ko kuma a’a.

Kafin hakan dai Saudiyya ta dau wasu matakai na dakile yaduwar cutar corona a cikin kasar da suka hada da dakatar da kai-kawo na jiragen sama da kuma hana sallar jam’i.

Kawo yanzu dai mutane 1,563 ne hukumomin na Saudiyya suka rawaito cewa sun kamu da cutar coronavirus a kasar, sai kuma 10 da suka rasa rayukansu.

 

3888447

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: dakata ، shirye-shirye ، saudiyya ، aikin hajji ، bana ، ministan ، kamfanin
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha