IQNA

Gwamnatin Tripoli Ta Ce Za Ta Kai Karar Dakarun Haftar A Kotun Duniya

23:51 - April 04, 2020
Lambar Labari: 3484679
Tehran (IQNA) gwamnatin kasar Libya mai mazauni a birnin Tripoli ta ce dole ne a gurfanar da su Haftar a kotun duniya.

Rahotanni daga kasar Liya na cewa, dakaru masu biyayya ga Halifa Haftar wanda kuma yake iko da gabashin kasar Libya ya kai hare-hare kan tashar jiragen sama ta birnin Tripoli a jiya Juma’a.

Gwamnatin hadin kan kasa tana cewa sojojin Halifa Haftar sun kai hare-hare kan tashar jiragen sama ne da makamai masu linzami a daren jiya wanda ya tilasta masu rufe ta.

Tun farkon watan Afrilun shekarar da ta gabata ce sojojin Halifa Haftar suka fara kokarin kwace birnin Tripoli daga hannun gwamnatin rikon kwarya ta Fa’iz Suraj.

Mutane dubu da dari biyar suka rasa rayukansu sannan wasu dubu shida suka ji rauni tun lokacin.

3889143

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Haftar ، Libya ، hare-hare ، birnin Tripoli ، lokacin ، rayukan ، gurfanar
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha