IQNA

23:56 - April 05, 2020
Lambar Labari: 3484681
Tehran (IQNA) kafofin yada labaran Saudiyya sun bayar da rahotanni kan halin dake ciki a kasar dangane da batun corona.

An bayar da rahotanni kan halin da ake ciki kan Corona a kasar Saudiyya dangane ad wadanda suka kamu da kuma wadanda suka warke.

A garuruwan Jidda mutane 124 sai kuma Makka 114 suka warke daga wanann cuta.

A birnin Riyadh Mutane 588 ne suka kamu da wannancuta yanain da uku daga cikinsu suka riga mu gidan gaskiya.

A jidda kuma mutane 218 ne suke dauke da cutar amma 4 daga cikinsu rasu, amma sauran ana ci gaba da kula da lafiyarsu a wurin da aka kebi a birnin domin kula da masu dauke da wannan cuta.

Ma'aikatar kiwon lafiya ta Saudiyya ta sanar da cewa, a halin yanzu an samu mutane sabbi da suke dauke da cutar da adadinsu ya kai 206 a fadin kasar, kuma Muhammad Al'ali kakakin ma'aikatar ya ce adadin jimillar mutanen da suka kamu ya zuwa yanzu ya kai dubu biyu 385 a kasar.

 

3889424

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: saudiyya ، adadin ، mutane ، corona ، ta kashe ، halin yanzu
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: