IQNA

Fitaccen Mai Fasahar Rubutun Kur’ani Dan Kasar Yemen Ya Rasu

13:18 - May 03, 2020
Lambar Labari: 3484758
Tehran (IQNA) sheikh Khamis Bin Mahfuz Huwaidi fitaccen mai fasahar rubutun kur’ani dan kasar Yemen ya rasu bayan kamuwa da corona.

Shafin yada labarai na tahdis net ya bayar da rahoton cewa, wannan fitaccen mai fasahar rubutun kur’ani ya rasu ne a birnin Maduna, kuma tuni kungiyar malaman musulmi ta duniya ta mika sakon ta’aziyyar rasuwarsa.

A cikin sakon nata kungiyar ta rubuta ayoyi na 27 zuwa 30 a cikin suratul fajr, da ke ishara da rai mai natsuwa yayin komawarta zuwa ga Ubangi madaukakin sarki a lokacin da Allah yake mai yarda da ita.

Sheikh Khamis Huwaidi ya rasu ne sakamakon kamuwa da cutar Corona a birnin Madina mai alfarma da ke Saudiyya, kuma ya rasu a jiya Asabar bayan jinya ta wani dan lokaci.

Ya bayar da gagarumar gudunawa wajen yada fasahar rubutun kur’ani mai tsarki da salon rubutu mai kyaun gaske mai kayatarwa, wanda ake nuna shi a dukkanin kasashen musulmi da ma kasashen duniya a tarukan baje kolin fasahar rubutu.

Wannan na a matsayin babban rashi da al’ummar musulmi suka yi na rasuwar sheikh Huwaidi a wannan lokaci da ake fama da wannan matsala ta annoba ta ta addabi duniya baki daya.

 

3895987

 

captcha