
Kamfanin dillancin labaran anatoli ya bayar da rahoton cewa, a jiya ne Omar Dogel Auglo fitaccen masani marubuci dan kasar Turkiya ya rasu sakamakon kamuwa da cutar corona a asibitin Pashak da ke kasar Turkiya yana da shekaru 52.
Ya shahara a kasar Turkiya a bangaren rubuce-rubucensa da kuma bayanan da yake gabatarwa a bangaren tarihin muslunci da kuma tarihin rayuwar manzon Allah.
Ya kasance daga cikin masu kaunar ahlul bait (AS) da kuma yada koyarwarsu a tsakanin al’ummar musulmi a kasar Turkiya, ta hanyar gidajen talabijin musammana cikin watan Ramadan.
Rajab Tayyib Erdogan shugaban kasar Turkiya ya aike da sakon ta’aziyya, tare da bayyana rasuwarsa a matsayin wani babban rashi ga dukkanin al’ummar kasar.