IQNA

23:03 - May 07, 2020
Lambar Labari: 3484774
Tehran (IQNA) fararen hula hudu ne su ka yi shahada a kasar Yemen, a wani hari da jiragen yaki na kawancen Saudiyya.

Tashar talabijin din al-Masirah ta kasar Yemen, ta ambato majiyar tsaron kasar tana cewa Harin da jiragen yakin kawancen Saudiyya su ka kai a yankin Abas, da ke gundumar Hajjah, ya yi sanadin shahadar mutane hudu daga cikinsu hadda jariri.

A ranar shida  ga watan Afrilun da ya shude ma dai, jiragen yakin kawancen a Saudiyya sun kai kwatankwacin wannan harin,a garin Jar da ke gundumar Abas wanda ya shafi fararen hula.

Tun a shekarar dubu das ha biyar ne dai Saudiyya ta shelanta yaki akan kasar Yemen, wanda ya zuwa yanzu ya ci dubban rayuka da kuma jikkata wasu dubun dubata. Bugu da kari,wasu dubun dubatar mutanen kasar sun zama ‘yan gudun hijira saboda rusa matsugunansu.

Har ila yau, hare-haren na Saudiyya sun yi sanadiyyar lalata asibitoci da kuma cibiyoyin kiwon lafiya a fadin kasar ta Yemen.

3897077

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Yemen ، kawancen saudiyya ، hare-hare ، ruwan wuta ، fararen hula ، kashe
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: